Gwamnan Zamfara ya sanar da cewa maigadin makarantar Jangebe yana daya daga cikin wadanda aka hada kai dasu wurin sace yaran

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya ce ‘yammatan Jangebe sun bayyana cewa maigadinsu na makaranta yana daga cikin wadanda aka hada kai dasu aka sacesu.

A ranar Laraba da ta gabata ne Matawalle ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan Talabijin na Channels.

Sama da dalibai 270 ne aka sace a makarantar gwamnati da ke garin jangebe na karamar hukumar Talata-Mafara da ke Zamfara a watan Fabrairu. An sako su a ranar Talata.

A yayin da aka bukaci ya bayyana wadanda suka sace yaran, gwamnan yace ‘yan bindigan sun sanar da cewa har da maigadin suka hada baki.

Matawalle yace ana bincike a kan haka amma bai sanar da sauran wadanda aka hada kai dasu ba.

“Har da maigadin makarantar. Yaran sun sanar da hakan kuma sun ce bayan an sakesu, ‘yan bindigan sun ce su gaishe musu da maigadin makarantarsu,” yace.

“Sun kara da bayyana sunansa a matsayin wanda ya ce su zo a lokacin su kwashe yaran, don haka da hannunsa a ciki.

“Sun sanar da hakan a gaban kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, za a yi bincike a kan hakan sannan a gano dukkan wadanda ke da hannu a ciki.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: