Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko suwane ne ba sun sace matafiya guda biyu da yammacin ranar Asabar a yankin da ake kira Wasinmi, jihar Osun.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, matafiyan da lamarin ya faru da su na kan hanyar su ne ta zuwa yankin Ikere, na jihar ta Osun.

A lokacin da take bayani, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ta tabbatar da sun sami labarin faruwar lamarin.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, sun tura jami’an ‘yan sanda yankin da lamarin ya faru don gudanar da bincike.

Ta kuma kara da cewa, ya zuwa yanzun sun kama mutum uku da ake zargin suna da alaƙa da satar mutanen.

Sannan kuma zasu cigaba da bincike har sai sun kama waɗanda sukayi wannan aika-aika.

Kuma ta ƙara da cewa jami’an su na ‘yan sanda sun bazama neman waɗanda aka sace a duk inda suke.

Leave a Comment

%d bloggers like this: