Kungiyar Dattawan Arewacin Ƙasar nan ta ACF ta ce, matsalar tsaro ta tsananta a yankin arewacin Najeriya, tana mai kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ji tsoron Allah, sannan ya cika alkawuran da ya yi wa ‘yan kasar nan na samar da zaman lafiya.

Kungiyar ta bayyana cewa, shugaba Buhari ya fi kowa sanin laifin da ke tattare da rantsuwa da al-Kur’ani mai girma ba tare da cikawa ba.

Ƙungiyar ACF ta ce, ta damu matuka kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kashe al’umma a yankin arewacin Najeriya duk da ikirarin Ministan Kula da Ayyukan ‘Yan sanda da ke cewa, an ci galabar ‘yan bindigar.

A cikin sanarwar da ta fitar, ACF ta ce, tana wakiltar dimbin al’ummar arewacin Najeriya wajen isar da fushinsu ga shugaba Buhari da zummar ganin ya gaggauta daukar mataki.

ACF ta yi tur da sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma sace daliban Jami’ar Ahmadu Bello su tara.

Leave a Comment

%d bloggers like this: