Wata ‘yar Najeriya, Maryam Shehu, ta haddasa cece-kuce mai ban sha’awa game da yin rubutu da fasahar rubutun hannu a makarantu

Wata matashiya yar Najeriya, Maryam Shehu, ta baiwa mutane da yawa mamaki da kyakkyawan rubutunta yayin da ta nemi wanda yake ganin ya isa su zo suyi gasa.

A wani sako da ta wallafa a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, budurwar ta sanya ɗaya daga cikin litattafanta na makaranta don nuna baiwar da Allah ya yi mata na iya rubutu.
Wasu mabiya shafin Twitter da suke ganin suma gwanaye ne a wajen rubutu suma sun wallafa nasu.

Lokacin da mutane suka ce lamarin zai sha bamban idan ana karanto mata tana rubutawa, sai budurwar ta nuna musu ba haka ba inda ta sake wallafa hoton wani rubutun nata.

matasaradio.com ta daukko wasu daga cikin sharshin mabiyanta :

@unilorinamebor ya ce: “Baba wai a inda kuke samun irin wannan kyawawan rubutu a koda yaushe. Ni nawa kamar tsuntsu na caccakar ƙasa.”

@lukmanadeola2 ya ce: “Zan so in ga rubutunki a lokacin da malamin makarantar sakandaren da ke jin yunwa ke karanto maki jawabai kina rubutawa.”

@Nigerianbreed20 ya ce: “Na tabbata ba rubutun ana fada kina rubutawa bane! saboda rubutunki ba zai kyan wannan ba yayin da malami ke fada kina rubutawa…. Ko yaya dai yayi kyau!”

Leave a Comment

%d bloggers like this: