Wani bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta wanda aka ga wata mata da tsohon ciki a titin Turai tana jan wani mutum da cewa shine yayi mata cikin da yake jikinta.

Duk da yadda ta dage tana cusa masa cikin, amma mutumin ya murje idanunsa yace sam ba nashi bane.

Matar ta dage a tsakar titi tana cacar baki a gaban jama’a tana cewa tabbas shine yayi mata cikin.

Duk da ya ki amincewa, ta ce baza ta taba sakin shi ba har sai ya tabbatar wa da kowa cewa cikinsa ne, The Nation ta ruwaito.

Wata mata ta shiga al’amarin dumu-dumu kamar yadda aka gani a bidiyon, tana cewa ya kamata mutumin ya yarda da cewa shi ya dirka mata cikin.

Ya tsoratar da matar cewa zai kira mata ‘yan sanda don ya ga wandunan wasu maza a gidansa, hakan ce tasa yake tunanin ba cikinsa bane.

Leave a Comment

%d bloggers like this: