Gwamnatin Najeriya ta ƙirƙiro da hanyoyi da dama domin rage raɗaɗin da annobar COVID19 ta jefa ɗai-ɗaikun yan Najeriya da kuma yan kasuwa

Kamar yadda muka sani gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro da sabbin tsare-tsare don rage raɗaɗin da annobar COVID19 ta jefa yan Najeriya a ciki.

Sai-dai duk da haka wasu daga cikin yan Najeriya na cikin duhu kan ko sun cancanta su shiga ɗaya daga cikin tsare-tsaren ko basu cancanta ba.

Zamu maida hankali ne akan shirin da babban bankin ƙasa CBN ya fito dashi na TCF, kuma zamu bayyana rukunin yan najeriyan da suka cancanta su shiga tsarin bada tancen.

Kamar yadda aka bayyana a kwanakin baya, CBN ya ƙirkiro shirin TCF ne a matsayin wani ƙunshi da zai taimaka wajen rage raɗaɗin da annobar korona ta haifar wa yan Najeriya.

CBN ya ware maƙudan kuɗaɗe kimanin 50 biliyan domin ƙunshin da farko, wanda bankin Microfinance ya rabawa yan Najeriya.

Rukunin yan Najeriya uku da suka cancanta su nemi rancen:

1. Magidanta

A jawabin bankin Microfinance, Magidanta yan Najeriya da suke da ƙwaƙƙwarar hujjar da zata nuna annobar ta shafi rayuwarsu, sun cancanci su nemi rancen.

2. Masana’antu.

Hakanan, masan’antun Najeriya suna da damar neman rancen amma sai suna da shaidar da aka amince da ita a hukumance da zasu nuna cewa annobar ta shafi ayyukan masana’antun su.

3. Ƙanana da matsakaitan masana’antu.

Ƙanana da matsakaitan masana’antu dake da tsari da banki suna da damar da zasu yi amfani da ita wajen neman rancen TCF ɗin.

Kamar yadda bankin Micrifinance ya bayyana, yan Najeriya ka iya amfana da kimanin 25 miliyan daga farkon ƙunshin.

 

 

1 Comment

  • Posted April 14, 2021 1:49 am 0Likes
    Aliyu Ahmad Usman

    Ina Nima tai MA ko

Leave a Comment

%d bloggers like this: