Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna tace a ranar Lahadi jami’anta sun bankado wani yukurin garkuwa da aka yi da wasu mutum biyar kuma ta ceto su.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.

“Rundunar na sanar da jama’a cewa tana matukar kokari wurin tabbatar da ta shawo kan matsalar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, satar shanu da fashi da makami a jihar kuma tana samun nasarori,” Jalige yace.

Kamar yadda yace, “A ranar 26 ga watan Maris wurin karfe 12 na rana labarai suka same mu na cewa ‘yan bindiga 10 dauke da makamai sun rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari kuma suna kokarin kwashe fasinjojin wata mota kirar Golf mai lamba DKA 539 TU dake tafiya Birnin Gwari zuwa Kaduna.

“Daga samun rahoton, rundunar sintirin dake yankin Buruku ta fara aiki. Sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan kuma cike da nasara suka fatattakesu da miyagun raunika tare da ceto mutanen.

“A halin yanzu jami’an tsaron na tsananta neman ‘yan bindigan don cafke su,” yace.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yace tuni wadanda aka yi yunkurin sacewan suka sadu da ‘yan uwansu.

Leave a Comment

%d bloggers like this: