Wani matashi mai suna Ryan Shelton wanda keda shekaru 29, ya wanke kafa ya gudu ya bar gari tare da mahaifiyar budurwarsa bayan budurwar ta sa ta haifa ma sa jinjirin, The Nation ta ruwaito.

Budurwar ta sa Jesse Aldridge, mai shekaru 24, its ce ta bayyanawa jaridar The Sun mamakinta na faruwar wannan lamari.

Jesse ta bayyana cewar saurayin na ta ya ci amanarta a yayin da take da tsohon ciki lokacin su na zaune tare da mahaifiyarta da mijinta mai suna Eric.
Ta kuma ce lamarin ya samo asali ne sadda su ka tare a gidan mahaifiyarta, a yayin da mahaifiyarta ta fara caka-caka da Ryan.

Kawai ranar da ta dawo gida da santalelen jinjiri, sai ta tarar da sun gudu tare sun koma wani gidan wanda nisan sa ya kai mil 30.

Jesse ta ce “mun kasance cikin zaman kulle a gida na tsawon lokaci wanda ban ji dadin zaman ba sakamakon yadda saurayina da mahaifiyata su ke yawan wasan banza. Kamata ya yi ace ta so jikokinta ta kuma nuna ma su kulawa ba wai ta je ta na wasanni da saurayina ba.”

Rahoto ya nuna cewar Ryan ya yanke alakarsu ne bayan ta haifa ma sa jinjirin a inda ya bayyana ma ta cewar shi ba zai iya cigaba da soyayya da ita ba. Ita kuwa mahaifiyarta cewa ta yi “dan adam ba shi da ikon hana ran sa abun da ya ke so”

Leave a Comment

%d bloggers like this: