Dirakta Janar na Ofishin manajin basussukan Najeriya DMO, Patience Oniha, ta ce basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yanzu ya kai N33.63 trillion.

A jawaban da ta saki a shafin sadarwanta na Tuwita, Oniha ta ce jita-jitan da ake yadawa kan adadin bashin da ake bin Najeriya yasa ta wallafa jerin basussuka.

A cewarta, “yana da muhimmanci in fayyace cewa wannan bashin na gwamnatin tarayya ne, birnin tarayya, da jihohin Najeriya 36,”

“Bashin ba na gwamnatin tarayya bane kadai, gwamnonin jihohi da birnin tarayya na karban bashi.”

“A bangaren gwamnatin tarayya, adadin bashin da aka karba ya karu ne saboda fadin farashin danyen mai a 2015.”

“Amma a kasafin kudin 2018 zuwa 2020, adadin basussukan sun ragu.”

“Abin takaici, illar annobar COVID-19 kan kudin shiga ya sabbaba tashin basussukan.”

Za ku tuna cewa a karshen shekarar 2020, DMO ta ce bashin da ake bin Najeriya ya kai N32.9tr.

Leave a Comment

%d bloggers like this: