Tsohon gwamnan jahar Sokoto Attahiru Bafarawa yayi wata ganawa ta mussaman da Kakakin Majalisar Tarayya na Kasa Femi Gbajabiamila a ofishinsa dake Abuja don tattauna matsalolin tsaro da kuma gabatar da bukatar biyan diyya ga wadanda bala’in kisan gilla da sace jama’a ya shafa a Arewacin Najeriya.

Bafarawa wanda ya baiyana ma Kakakin Majalisar tarayya cewar lokaci yayi da ya kamata a dauki mataki na baiwa al’ummar da bala’in ya shafa agaji da kuma fito da babying a wannan matsalar da gaggawa.

Bafarawa ya mika ma Kakakin Majalisar dimbin takardu dake dauke da sunaye da kadarori na wasu da suka yi hasara a sakamakon hare hare da kisan gillar a lokuta dabam dabam a Arewacin Najeriya.

A jawanbinsa Kakakin Majalisar Hon Femi Gbajabiamila ya jijjina na tsohon gwamna Bafarawa dangane da wannan da namijin kokarin da yayi na hada bayanai masu wuya akan wadanda suka fuskanci matsalar rayuwa ko rasa yan uwa da hasara.

Yace, zai duba bukatun Gidauniyar Ta Bafarawa tare da wadanda suke da hakkoki akan lamarin bayar da shawarwari don daikar matakin da ya dace.

Ya kuma yi godiya ga wannan ziyara tare da tabbatar ma tsohon gwamnan da tawagarsa da ci gaba da hadin kai don ciyar da kasa gaba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: