Ministan Sadarwar ƙasar nan, Isa Pantami,ya ƙara jaddada matsayarsa kan kulle duk wani layin waya da ba’a haɗa shi da NIN ba

Ministan sadarwa na ƙasar nan, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya gargaɗi yan Najeriya waɗanda har yanzun ba su haɗa layukan wayar su da NIN ba da suyi gaggawar yi.

Ministan ya ce babu gudu ba ja da baya, dan haka kowa ya gaggauta haɗa nashi tun kafin lokaci yayi.

Isa Pantami ya faɗi haka ne a wasu zafafan sakonni da ya aike a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita ya yin da yake martani kan zargin da wasu jaridu ke masa da hannu a Boko Haram.

Ministan ya ce babu wasu yan shaci-faɗi da wasu tsirarun mutane za su mishi barazana da shi da zai iya dakatar da shi gudanar da ƙudirin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A saƙon da ya saki wanda ya yi magana kan NIN, Pantami ya ce:

“Idan baka haɗa layin ka da lambar jikin katin ɗan ƙasa ba wato NIN, to ka gaggauta yi kafin mu ɗauki mataki na gaba. Yan ta’adda sun fara shan wahala da matakin da muka ɗauka.”

Ya kuma ƙara da cewa ba gudu ba ja da baya kan kudirin gwamnati na sanƙame duk wani layin waya da ba’a haɗa shi da NIN ba don yaƙar matsalar tsaro.

“Akan lamarin haɗa layin waya da NIN don yaƙar rashin tsaro, ba gudu ba ja da baya. Buƙatar mu a ɓangaren gwamnati kamar yadɗa kundin tsarin mulki kasa ya tanadar a sashi na 14 (2) shine samar da tsaro.”

Ba tattalin arziƙi ƙadai muka sa agaba ba, tabbas ba gudu ba ja da baya kuma b wanda ya is ya hana mu, don haka masu ɗaukar nauyin ta’addancin su cigaba,” Pantami ya jaddada.

Leave a Comment

%d bloggers like this: