Yarima Abdullah bin Mosaad na kasar Saudiyya zai siya kungiyar kwallon kafa ta Chateauroux a kasar Faransa.

kudi’, Yarima Abdullah bin Mosaad yana dab da mallakar kungiyar kasar Faransa ta Chateauroux, The Punch ta ruwaito.

Yariman wanda ya mallaki kungiyoyin Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United a Indiya da Al Hilal United a UAE yana daf da kara sabuwar kungiya kan wadanda ya ke da su.

“Mun dade muna sha’awar Chateauroux, muna yi nisa da tattaunawa,” Yarima Abdullahi ya shaidawa AFP cikin hirar Zoom.

“Kungiyar na cikin mayucin hali a mataki na biyu amma ina sa ran za ta farfado a nan gaba.”

A halin yanzu Chateauroux tana kasar tebur na gasar kwallon kafa na Faransa inda ta samu nasarori hudu cikin wasanni 28 da ta buga.

Akwai yiwuwar za ta iya fadawa mataki na uku.

Yariman, wanda ya taba jagorancin bangaren wasanni a gwamnatin Saudiyya ya bada umurnin a siya masa kungiyar ta Chateauroux don hada ta cikin jerin kungiyoyin da ya mallaka.

“Ina kaunar wasanni da kudi,” in ji Yariman mai shekaru 56 da aka kiyasta arzikinsa $240,000 miliyan.

“A lokacin da na saka hannun jari a Ingila da Belgium, na yi farin ciki. Amma Faransa daban ne saboda kasar na tuna min kuruciya ta.

“Akwai ababe da yawa da na ke tunawa a kasar da dan uwa na (yarima) Abdulrahman a can aka haife shi.

“Na san Chateauroux babu nisa daga Paris (kimanin kilomita 270) wani dalilin da zai sa in yi farin ciki idan na tafi Faransa bayan zuwa wurin cin abinci, shan shayi da wurin mike kafa.”

Leave a Comment

%d bloggers like this: