Matashiya haifafar jihar Kano ta ƙera manhajar android na kai rahoton fyaɗe.

Wata matashiya haifafar jihar Kano, Saadat Aliyu ta ƙera manhajar android mai suna ‘Helpio App’ domin kai rahoto kan fyaɗe, Channels Television ta ruwaito.

An kaɗamar da ‘Helpio App’ a playstore a ranar 6 ga watan Agustan 2020.

Saadat Aliyu wacce ta kafa Shamrock Innovations, cibiyar Fasaha ta Mata da Matasa a Kano ta ce kowa na iya zuwa Playstore ya sauke manhajar a wayarsa.

“Za ka iya zuwa Playstore, ka nemo shi sannan ka sauke sai ka yi rajista da imel ɗin ka cikin harshen Hausa ko Ingilishi,” kamar yadda ta shaidawa Channels Television a ranar Litinin.

“Kawo yanzu kuna wayarka. Daga nangiyar tallafawa wadanda aka ci zarafinsu, marayu da marasa galihu (ISSOL) da wata ƙungiyar na tallafawa gajiyayu, kare hakkin yara da walwalarsu (EDCRAW) sun yi rajista a manhajar.”

Ta ce ta fara koyon fasahar sadarwa ne daga wurin ɗan uwanta a lokacin tana ajin ƙaramar sakandare daga bisani ta koya da kanta har ta zama mai ƙera manhaja

Matashiyar ta ce nan ba da dadewa ba za ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar ta mai alaka da fasaha da kuɗi da ake fatan zai taimakawa mata da sauran jama’a.

Leave a Comment

%d bloggers like this: