Rundunar sojin saman Najeriya sun yi arangama da gagararrun ‘yan bindiga a wani samame da suka kai a Kaduna

Wani sojan sama na Najeriya ya rasu sakamakon artabu da ‘yan bindiga a jihar Kaduna. Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Ya sanar da yadda ‘yan bindigan suka kashe Abubakar Muhammad Ahmad tare da wasu abokan aikinsa a babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Sani ya bayyana cewa sojan na shirye-shiryen aurensa a makonni uku masu zuwa.

 

Leave a Comment

%d bloggers like this: