Sojojin Najeriya sun bazama neman matuƙan jirgin sama da suka ɓata bayan an nemi wani jirgin yaƙi sama ko ƙasa ba a gani ba bayan jirgin ya tafka hatsari a dajin Sambisa dake arewa maso gabas na Najeriya.

HumAngle ta fahimci yadda sojojin suka rikice suna neman sojojin lungu da saƙon dajin Sambisa.

Yanzu haka an zarce sa’o’i 24 tun bayan faruwar lamarin.

Dajin Sambisa babban daji ne wanda yankin Boko Haram ɗin Sheƙau suka mamaye shi kuma ana zargin sune suka kaiwa jirgin farmaki.

Kamar yadda sojojin saman Najeriya suka sanar a takarda ranar Laraba, an rasa inda jirgin saman yake bayan fita ayyukan yau da kullum da yayi domin taimakawa dakarun sojin kasa.

An gano cewa aikin yana daga cikin kokarin dakarun na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso gabas.

Kamar yadda PRNigeria ta sanar, an ga jirgin yana yawo kusa da kauyukan Kurmiri da Njimia bayan ya ragargaji ‘yan ta’adda a yankin Sambisa.

Kauyen Njimia dake kusa da dajin Sambisa na fuskantar aikin dakarun sojin saman da na kasa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: