Wasu mutane dauke da bindigu a safiyar ranar Juma’a sun afka gidan dan kwallon kafa, Chris Smalling, sun yi masa fashi da iyalansa da yaransa a gidansa da ke kasar Italy, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahotanni, dan wasan yana cikin gidansa da matarsa da dansa mai shekaru uku a lokacin da mutanen sanye da takunkumin fuska suka kutsa gidan suka tilasta shi ya bude musu wurin da ya ke ajiye kaya masu muhimanci.

Sun tilastawa Smalling mika musu agogonsa na alfarma kirar Rolex da wasu kaya masu muhimmanci daga wurin ajiyar.

Matar Smalling, Sam, ta kira yan sanda misalin karfe 5 na asuba kuma daga bisani yan sandan sun isa gidan dan kwallon da ke mil 25 kudu da birnin Rome.

A halin yanzu yan sanda na cigaba da bincike a kan lamarin kuma Roma ta ce za ta tallafawa dan wasan.

Yana zaune ne tare da matarsa yar asalin birnin Manchester. Sun yi aure tun Yunin shekarar 2017 sannan suka haifi dansu na farko, Leo, daf da dawowarsu babban birnin na Italy.

Mai tsaron bayan ya kasance yana buga wa wasa a Rome tun bazarar 2019.

Leave a Comment

%d bloggers like this: