Bayan zaman awanni takwas da gwamnatin tarayya ranar Juma’a, da yiwuwan kungiyar Likitoci NARD za ta janye yajin aikin a yau Asabar.

A cewar ThePunch, an samu labari daga ganawar da suka yi tun daga karfe 3 na rana zuwa 11 na dare ranar Juma’a cewa bangarorin biyu sun samu matsaya kuma sun rattafa hannayensu kan yarjejeniya.

Wata majiya ta ce Likitocin sun amince zasu janye yajin aikin da aka kwashe kwanaki tara yanzu anayi idan shugabannin kungiyarsu suka amince.

Wakilan Likitocin sun yi alkawarin ganawa da mambobinsu ranar Asabar, sannan su yanke shawara.

“An samu matsaya a ganawar kuma Likitocin sun amince da abubuwan da akayi na amsa bukatunsu. Saboda haka za su gana da mambobinsu ranar Asabar kuma su yanke shawara kan yajin aikin,” majiyar tace.

Da farko, Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi iyakan kokarinta wajen amsa bukatun Likitocin guda bakwai.

Hakazalika kwamitin kiwon lafiya na majalisar wakilai ta zanna da Likitocin don rokonsu su janye yajin aiki don rayuwar talakawan dake kwance a asibitocin gwamnatin kuma ba za su iya zuwa na kudi ba.

Shugaban kwamitin, Tanko Sununu, yayin hira da manema labarai bayan zaman ya ce Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, zai gana da Likitocin ranar Talata.

Leave a Comment

%d bloggers like this: