Wata ’yar kasuwa mai amfani da dandalin sada zumunta na Twitter mai suna Temi Giwa-Tubosin, ta sanya gasar kwaikwayon daurin dankwalin tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonja-Iweala.

Ms Giwa-Tubson ta wallafa sakon sanya gasar ne a shafinta na Twitter, inda ta daurin kallabi irin na tsohuwar minister sannan kuma tana jawabi a kan tattalin arziki kamar yadda aka san Ngozi da yi.

Temi ta yi alkawari bayar da kyautar naira dubu dari ga duk wanda ya fi dacewa da kwaikwayon daurin dankwalin tsohuwar minister.

Da dama daga cikin mabiya shafin na Twitter, suna ci gaba da aika hotunansu da daurin kallabi a kokarinsu na kwaikwayon tsohuwar minister kudi da ta yi zamani a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Al’ummar Najeriya da dama da kuma na kasashin Afrika har ma da na ketare, na ci gaba da bayyana alfaharinsu da nuna goyon bayan a kan Ms Ngozi, mace ta farko da ake sa ran za ta zama Shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya.

Leave a Comment

%d bloggers like this: