Rundunar ‘yan sanda a ranar Talata ta damke wata kungiyar masu laifi 9 dake siyar da bindigogi kala-kala ga ‘yan bindigan daji, masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauransu.

Daga cikin wadanda ake zargin kuma aka kama, akwai wani mai suna Anthony Base, wanda aka kama, aka gurfanar sannan aka kai shi gidan yari saboda wannan laifin amma sai wani gwamnan arewa maso yamma yayi masa rangwame aka sako shi.

A yayin da aka kai wadanda ake zargin tsohuwar hedkwatar sashi na musamman dake yaki da fashi da makami a Abuja, kakakin rundunar, Frank Mba, ya koka da yadda makamai da miyagun kwayoyi ke yawo a kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa, ya jaddada cewa jami’an FIB, STS da rundunar IGP ta IRT, karkasin umarnin CP Abba Kyari da DCP Kolo Yusuf ba za su tsagaita ba a farautar masu laifi.

Mba ya bayyana cewa, an samu miyagun makamai 10, harsasai 2,496, kwalayen Tramadol wadanda za su kai darajar miliyan 3, buhunan wiwi, naura mai kwakwalwa 2, wayoyi 8 da mota kirar Golf daya wacce ke kai da kawowa ‘yan bindiga makamai.

Leave a Comment

%d bloggers like this: