Yan Arewa sun fara kaura daga jihar Imo sakamakon harin da ake kai musu.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an sake kai hari kan yan Arewa mazauna jihar Imo inda aka hallaka akalla mutum bakwai.

A cewar rahoton, wannan sabon harin ya auku ne makon da ya gabata inda aka kashe mutum hudu a Orlu kuma mutum uku a garin Amaka.

Wani mazaunin Owerri, Dr. Lawan Yusuf, ya bayyana cewa yan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ne suka kai harin.

“Ko jiya yan IPOB sun kaiwa wasu yan Arewa mahauta hari kuma sun kashe mutum uku. Mun ji jana’izarsu,” yace.

“Duk lokacin da suka hadu da yan Arewa a wurare kasuwancinsu, su kan tambayesu shine an basu izinin zama a kasar Biyafara, idan suka ce a’a, sai su lallasa mutum da makamansu; an kashe mutanenmu da dama ta haka.”

Yusuf ya ce an tura jami’an tsaro wuraren da yan Arewa suka fi yawa ne “amma babu jami’an tsaro a wasu wuraren kuma cikin tsoro muke rayuwa.”

Cikin makonni biyu da suka gabata yanzu, an hallaka akalla yan Arewa 11 a jihar Imo.

Leave a Comment

%d bloggers like this: