Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wasu sauye-sauye a dokokin shari’ar Musuluncin ƙasar inda ta halasta shan giya da yin zina.

Sauyin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da daukar hankulan masu zuwa yawon bude ido musamman daga kasashen Yamma.

Ƙasar na fatan kwaskwarimar za ta habaka tattalin arzikinta tare da nuna wa duniya cewa ita kasa ce mai sassaucin ra’ayi, karbar sauyi da kuma tafiya da zamani.

Sanarwar ta biyo wata matsayar da kasar ta dauka mai cike da tarihi ta dawo da huldar jakadanci da kasar Isra’ila, wacce ita ma ake sa ran za ta kara yawan masu yawon bude ido da zuba jari.

Canjin ya soke hukuncin da aka tanada ga masu shan giya, sayenta ko mallakarta ga ’yan shekara 21 zuwa sama.

Ko da yake ana samun giya kusan a dukkan mashaya da wuraren shakatawar biranen kasar, a baya mutane na bukatar lasisin gwamnati domin sayarwa, jigila ko kuma shan giyar.

Sabuwar dokar za ta kyale Musulmai wadanda a baya aka haramta wa mallakar lasissin giya su iya shan giya ba tare da wani tarnaki ba.

Kazalika dokar ta halastawa marasa aure su ci gaba da mu’amalar da auratayya da juna, ta fuskar zina da sheƙe aya.

To sai dai sauran dokokin Musulunci za su ci gaba da kasancewa a dukkannin yankuna bakwai da suka hada Daular.

Kwaskwarimar dokokin shari’ar na zuwa ne lokacin da kasar ke dab da karbar bakuncin akalla mutum miliyan 25 domin bikin World Expo, bayan da annobar COVID-19 ta kawo mata tsaiko.

 

Kakaki24

Leave a Comment

%d bloggers like this: