Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kafa kwamiti na bincike kan wani jami’in ta da ake zargi da kwartanci da matar aure

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kafa kwamiti mai mutum biyar domin fara bincike kan jami’inta, Sani Rimo, wanda aka ce an kama shi da matar aure a cikin dakin Otel a Kano.

Babban Kwamandan Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya tabbatar da cewa an bawa kwamitin wa’adin kwanaki uku ta yi bincike kan lamarin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Na kafa kwamitin bincike na kuma na bata wa’adin kwanaki 3 domin ta bata rahoton ta. Na kuma gayyaci bangarorin da abin ya shafa domin su bada ba’asi

“Hisbah tana da dokokin ta, kuma idan muka same shi da laifi, za mu dauki matakin da ya dace a kansa bisa yadda dakokin mu suka tanada,” in ji shi.

Rahotanni sun ce dan sanda daga ofishin Noman’s Land ne ya kama Mista Rimo a dakin wani otel a yankin Sabon Gari da ke Kano.

Majiyoyi daga rundunar yan sanda sun ce sun samu rahotanni ne game da shi sannan suka garzaya suka kama shi tare da matar a dakin.

A baya Mista Rimo shine jami’in tawagar yaki da masu karuwanci na hukumar ta Hisbah wanda karuwai ke shakkarsa sosai a yankin na sabon gari.

A halin yanzu shine jami’in da ke kula da sashin masu hana bara a Kano.

Kawo yanzu yan sanda ba su yi martani kan lamarin ba.

Leave a Comment

%d bloggers like this: