An buɗe wa mata damar shiga aikin soja a Kwalejin Tsaro ta King Fahd da ke Riyadh a Saudiyya.

Jaridar Saudi Gazette ta ƙasar ta ce za a fara karɓar takardun mata masu son shiga aikin soja daga 13 ga Fabrairu zuwa 18 ga Fabrairun wannan shekarar, kamar yadda hukumar da ke kula da harkokin soja ƙarƙashi ma’aikatar harkokin cikin gida ta sanar.

Kwalejin Tsaro ta King Fahd makaranta ce ta koyon aikin soja da ke babban birnin Saudiyya, Riyadh.

Ɗaliban da suka kammala karatu a wannan makaranta na iya samun aiki a bangarorin tsaro da dama na ƙasar.

Wuraren sun haɗa da ma’aikatar harkokin cikin gida da hukumomin da ke sa ido kan safarar ƙwayoyi da rundunar tsaro ta civil defense da hukumar shige da fice da ta gidan yari da dai sauran su,
Tun bayan da Yarima Mohammed Bn Salman ya zama yarima mai jiran gadon Masarautar Saudiyya a shekarar 2017, ya fara kawo sauye-sauye da dama da yin garanbawul a fannonin da suka shafi tattalin arziki da kuma nishaɗi.

Sai dai yariman na shan suka daga wajen wasu da suke ganin yana so yi yi karan tsaye ne ga dokokin da addini da al’ada suka yarda da su.

Ya kawo sauye-sauye kamar bai wa mata ƴancin tuƙa mota, da ba su damar zuwa filayen wasa don kallon wasannin ƙwallo da na dambe.

Sannan ya yi ta bai wa mawaƙan ƙasashen yamma izinin shiga ƙasar don inganta ɓangaren nishaɗi.

Leave a Comment

%d bloggers like this: