Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International tace dakarun Etritrea sun yiwa daruruwan fararen hula kisan gilla a Tigray mai fama da rikicin ‘yan tawayen TPLF, yankin da suka yi iyaka da shi daga bangaren arewacin Habasha.

Cikin rahoton da ta fitar a ranar Juma’a 26 ga watan Fabarairu, Amnesty ta bayyana kisan gillar a matsayin ta’asa babba da ka iya zama laifin yaki.

Amnesty tace ta tattara hujjojinta ne bayan ganawa da wasu daga cikin fararen hular da suka tsira daga kisan gillar dakarun kasar ta Eritrea su 41, sai kuma hotunan da ta samu daga tauraron dan adam, wadanda suka nuna yankunan da aka tafka mummunar ta’asar.

Sai dai ministan yada labaran Eritrea Yemane Gebremeskel yayi watsi da rahoton, wanda ya bayyana a matsayin yunkuri na shafawa kasarsa kashin kaji.

Tun cikin watan Nuwamba ake gwabza fada tsakanin sojojin Habasha da ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray, bayan da Fira Minista Abiy Ahmad ya bada umarnin afka musu, bayan da suka kaddamar da farmaki kan sansanonin sojojin kasar.

Leave a Comment

%d bloggers like this: