Jaridar Punch ta ce babban kotun tarayya da ke Legas ya hana gwamnatin tarayya toshe layukan wayoyi watau SIM da ba ayi masu rajistar lambar NIN ba.

Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta bada umarni ta hannun hukumar NCC, ta bukaci kamfanoni su rufe duk wani layin wayar da bai da lambar NIN.

Wannan mataki da NCC ta dauka ya sa tsohon mataimakin shugaban kungiyar NBA na kasa, Monday Ubani, ya kai kara kotu, ya na kalubalantar gwamnati.

Babban lauya Monday Ubani ya nemi a hana NCC toshe layukan da ba a hada su da lambar ta NIN ba.

A karshe Alkali M.A Onyetenu ya yanke hukunci cewa a tsawaita wa’adin da watanni biyu daga ranar da aka zartar da hukunci, ya ce wa’adin da aka sa ya kure.

Mai shari’a Onyetenu ya karbi kukan lauyan, ya ce kokarin yin rajistar NIN cikin wahala, zai ci karo da sashe na 39 da 41 na tsarin mulki a kan damar ‘yan kasa.

Alkalin ya kuma ce tursasa wa mutane har miliyan 200 yin rajistar lambar NIN ta ‘yan kasa a lokacin da ake fama da annobar COVID-19, zai jefa jama’a cikin hadari.

Kwanaki kun ji yadda Hukumar sadarwan Najeriya, watau NCC ta umurci dukkannin kamfanonin sadarwa su dakatar da rijistar sababbin layukan waya.

NCC ta bada wannan umurnin ne saboda manufar gwamnatin tarayya na duba rumbun wadanda su kayi rajista da kuma tabbatar da cewa kamfanonin na bin dokoki.

Leave a Comment

%d bloggers like this: