Ana cigaba da zaman dar-dar a jihar Imo a yayin da yan bindiga a safiyar ranar Alhamis suka kai hari hedkwatan ‘yan sanda da ke Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli.

Ana cigaba da zaman dar-dar a jihar Imo a yayin da yan bindiga a safiyar ranar Alhamis suka kai hari hedkwatan ‘yan sanda da ke Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli, The Punch ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ce wani mazaunin Mbieri ya shaida masa cewa yan bindigan sun kai hari misalin karfe daya na daren nan take suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.

Ya ce yan bindigan sun kuma sace wayoyin salula mallakar wadanda ake tsare da su da na yan sandan da ke ofishin.

Amma majiya daga ofishin yan sanda ta shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa yan sandan da ke kan aiki sun dakile harin da yan bindigan suka yi niyyar kai wa.

Dan sandan ya ce, “Mun fafata da su amma sun fi karfin mu. Makamansu sun fi namu. Sun sace dukkan wayoyin da suka gani a nan, sannan sun saki dukkan wadanda ake tsare da su sun lalata ginin ofishin mu.”

Majiyar ya ce maharan sun sace dan sanda daya sun kuma raunta wasu jami’n.

Leave a Comment

%d bloggers like this: