Ƙungiyar IMN ta ƴan shi’a mabiya Zakzaky ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka kan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara.

Cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Ibrahim Musa ya aika wa BBC ranar Lahadi ta ce ta yi imanin gwamnan ya ɗauki matakin ne sakamakon matsin lamba daga abin da ta kira “wasu malamai da ba su jituwa da malamin.”

Ta ce matakin haramta masa karatu da wa’azi ya saɓa wa ƙundin tsarin mulki da kuma dokokin ƙasashen duniya na keta haƙƙin ɗan Adam.

Gwamnatin Kano dai ta ɗauki matakin ne bayan samun umurnin kotu na rufe masallacin Sheikh Abduljabbar da kuma hana shi wa’azi.

Hakan ya ta so ne bayan zarginsa da yin kalaman da ka iya tunzura jama’a a cikin wa’azin da yake gabatarwa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: