Ƙungiyar ta ce mutum 78 ta kashe a harin a harin mafi muni a baya-bayan nan. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum 110 aka kashe, yayin da rundunar sojan Najeriya ta dage cewa 43 ne.

A safiyar Lahadi Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya jagoranci jana’izar mutum 43 kuma a lokacin mazauna yankin sun faɗa masa cewa ba su gama tantance yawan waɗanda suka mutu ba.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce akwai mata guda 10 da ke aiki a wata gonar shinkafa da suka ɓata biyo bayan harin.

BBC

Leave a Comment

%d bloggers like this: